Mawaki Burna Boy Ya Karbi Addinin Musulunci

Shahararren mawakin Najeriya, Damini Ogulu wanda aka fi sani da ‘Burna Boy’, ya bayyana cewa ya karɓi Musulunci bayan dogon lokaci yana nazari da neman gaskiya game da addini da manufar rayuwa.

A cewar Burna Boy, babu wanda ya tilasta masa sauya addini, sai dai ya samu nutsuwa da fahimtar gaskiya bayan zurfin tunani.

“Na yi bincike kan addinai da yawa, ina tambayar kaina menene gaskiya game da rayuwa. A ƙarshe zuciyata ta samu natsuwa da Musulunci, don haka na karɓe shi,” in ji shi.

Mawakin ya ƙara da cewa yana mutunta dukkan addinai, kuma yana kira ga jama’a su zauna lafiya da juna, su guji rarrabuwa saboda addini ko ƙabila.

Burna Boy, wanda ya yi fice da wakoki kamar “Last Last” da “City Boys”, ya ce burinsa shi ne ya rayu cikin gaskiya da mutunci, ba wai don sunan addini kawai ba.

Comments (0)
Add Comment