Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wani mutum da ke kera Bam-bamai ga kungiyar IPOB

Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wani da ake zargin dan asalin kungiyayar dake fafutikar kafa kasar Biafra ne ta IPOB bisa zargin cewa yana kera Bam-bamai a wani samame da suka kai a Uba Umuaka da ke karamar hukumar Njaba a jihar Imo.

An kama wanda ake zargin ne mai shekaru 50, Simeon Onigbo ne ranar Alhamis.

Da yake tabbatar da kamun a yau, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar CSP Michael Abattam, ya ce wanda ake zargin da aka yi masa tambayoyi a nan take, ya amince da cewa shi ne ya kera yawancin na’urori masu fashewa da ake amfani da su wajen kai hari ga ofisoshin ‘yan sanda a jihar da kuma wajen jihar.

Ya kuma ce Sashen Kashe Bama-Bamai na Rundunar, sun karbe bam din da aka gano domin tantancewa da kuma yiwuwar tayar da su.

Comments (0)
Add Comment