Shugaba Buhari ya kaddamar da kwamitin gudanarwar kamfanin mai na NNPC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin gudanarwar kamfanin mai na kasa NNPC.

Da yake kaddamar da kwamitin karkashin jagorancin Sanata Margery Chuba Okadigbo a fadar shugaban kasa a yau a Abuja, shugaban kasar ya umarce su da su mayar da hankali wajen samun riba tare da gudanar da aiki daidai da takwarorinsu na kamfanonin man fetur a fadin duniya.

Shugaban kasar ya tunatar da ‘yan kwamitin cewa an samar da su ne a sakamakon sauye-sauyen da dokar masana’antar man fetur ta gabatar na neman mayar da harkar man fetur a Najeriya zuwa hannun ‘yan kasuwa da kuma bin kyakkyawan tsarin kasuwanci a duniya.

A nasa jawabin, karamin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya ce a karkashin wannan gwamnati an samu nasarori da dama a harkar man fetur da suka hada da sanya hannu kan dokar masana’antar man fetur, rajistar kamfanin NNPC da kuma kaddamar da kwamitin gudanarwar kamfanin NNPC.

Comments (0)
Add Comment