Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa bisa rasuwar tsohon shugaban Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano Farfesa Abdulhameed Isa Dutse.
Marigarayin ya yiwa gwamnatin jihar Jigawa aiki tsakanin watan Fabrairun 1992 zuwa Fabrairun 1994 a matsayin kwamishinan lafiya, daga baya kuma ya zama sakataren gwamnatin jiha a karkashin mulkin tsohon gwamna Ali Sa’adu Birninkudu.
Shugaban kasar ya bayyana rasuwar marigayi a matsayin babban rashi ga fannin kiwon lafiya.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
A sanarwar da Mallam Garba Shehu ya bayar a madadin shugaban kasa ta bayyana cewar rasuwar marigayi ta haifar da gibi ga yan Nigeria wajen cigaba da amfana da kwararrun likitocinta da suka sadaukar da rayuwarsu wajen bautawa al’umma.
Shugaba Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga Asibitin Aminu Kano da Gwamnatin Jihar Jigawa da kungiyar likitoci bisa rasuwar kwararren likitan tare da adduar Allah Ya jikansa kuma saka shi a gidan Aljanna.