Shugaba Buhari yayi amannar cewa tsarin ‘yansandan jihoshi ba shi zai haifar da da mai ido ba ga Najeriya ba

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi amannar cewa tsarin ‘yansandan jihoshi ba shi zai haifar da da mai ido ba ga kasarnan.

Shugaban kasar ya sanar da haka a wata fira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, wacce ake haskawa a halin yanzu.

Shugaban kasar ya kare matsayarsa da cewa akwai yiwuwar gwamnoni suyi amfani da yansandan jihoshi wajen cimma burinsu na siyasa.

Da yake magana akan yanayin tsaro a kasarnan, shugaban kasar yace dole sarakunan gargajiya su taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya a kauyukansu.

Ya kuma bukaci karin tattaunawa wajen magance rikicin manoma da makiyaya da ake samu a kasarnan.

A wani batun kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Sanata Magaret Chuba Okadigbo a matsayin shugabar kwamitin gudanarwar kamfanin man fetur na kasa (NNPC).

Magaret Okadigbo ta maye gurbin Ifeanyi Ararume, wanda shugaban kasar ya nada lokacin da aka kaddamar da kwamitin a ranar 19 ga watan Satumbar bara.

Comments (0)
Add Comment