Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken binciken ma’aikatun gwamnatin Tarayya

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken binciken ma’aikata da tantance gibin ƙwarewa a cikin dukkanin ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, domin ƙarfafa iya aiki da haɓaka ingancin hidimar gwamnati.

Shugaban ya bayyana haka ne jiya a birnin Abuja yayin bikin farko na makon Ma’aikatan Gwamnati na Duniya na shekarar 2025.

A cewarsa, dole ne a tabbatar da cewa kowane ma’aikaci na a inda ya dace da ƙwarewarsa, domin samun sahihin aikin gwamnati da ingantaccen sakamako ga al’umma.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci a kammala aikin cikin gaggawa don bayar da damar aiwatar da sauye-sauye, yana mai jaddada muhimmancin bayanai da ingancinsu wajen yanke shawarar manufofi bisa hujjoji da kuma gwada ci gaban Najeriya da ƙasashen duniya.

Comments (0)
Add Comment