Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken binciken ma’aikata da tantance gibin ƙwarewa a cikin dukkanin ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, domin ƙarfafa iya aiki da haɓaka ingancin hidimar gwamnati.
Shugaban ya bayyana haka ne jiya a birnin Abuja yayin bikin farko na makon Ma’aikatan Gwamnati na Duniya na shekarar 2025.
A cewarsa, dole ne a tabbatar da cewa kowane ma’aikaci na a inda ya dace da ƙwarewarsa, domin samun sahihin aikin gwamnati da ingantaccen sakamako ga al’umma.
Shugaba Tinubu ya kuma bukaci a kammala aikin cikin gaggawa don bayar da damar aiwatar da sauye-sauye, yana mai jaddada muhimmancin bayanai da ingancinsu wajen yanke shawarar manufofi bisa hujjoji da kuma gwada ci gaban Najeriya da ƙasashen duniya.