’Yan sanda sun kama wani matashi ake zargin ya kashe yayansa da matarsa, ta hanyar sauran su da adda yayin da suke barci a Jihar Kebbi.
Ana zargin matashin mai shekara 25 ya kai wa ma’auratan, Muhammed Haruna da matarsa Habiba hari da adda ne a ƙauyen Asarara da ke Gundumar Kimba a Ƙaramar Hukumar Jega ta jihar.
A cikin wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar, ta ce ana zargin wanda ake tuhumar ya sha yin barazana ga ma’auratan da adda a lokuta da dama kafin a kashe su.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umar M. Haɗejia, ya bayar da umarnin a miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike.