Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya ce Jam’iyyar APC a jihar a shirye take ta gudanar da sahihin zaɓen fid-da-gwani cikin gaskiya da adalci idan yunƙurin cimma matsaya kan ’yan takara kafin zaɓen 2027 ya gagara.
Buni ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan amincewa da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Mallam Wali, a matsayin ɗan takarar gwamna da jam’iyyar ta fi so.
A cewar gwamnan, zaɓen Wali ya biyo bayan matsayar da aka cimma a wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar 23 ga Afrilu, 2026.
“An amince da shi a matsayin wanda jam’iyyar ta fi so, amma idan ba a samu cikakkiyar yarjejeniya ba, za mu koma tsarin zaɓe,” in ji shi.
Gwamnan ya ce jam’iyyar ba ta kawar da yiwuwar gudanar da zaɓen fid-da-gwani kai tsaye ba domin zakulo ’yan takara domin mukamai daban-daban a jihar ba.
“Wannan ba sabon abu ba ne. A shekarar 2019, an tsayar da ni a matsayin ɗan takarar maslaha, amma wasu masu neman takara sun ƙalubalanci matakin, sai muka je zaɓe inda na zama ɗan takarar jam’iyya da gagarumin rinjaye. A shirye muke mu maimaita wannan tarihin idan ba a cimma matsaya ba,” a cewarsa.
Buni ya bayyana cewa har yanzu shugabannin jam’iyyar na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma masu neman takara domin samun mafita cikin lumana.
“Muna tattaunawa da juna tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ciki har da masu neman takara domin cimma mafita ta sulhu,” in ji shi.
Gwamnan ya jaddada cewa haɗin kai a cikin jam’iyyar shi ne babban abin da ya sa a gaba, yana mai cewa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ’ya’yan APC na da matuƙar muhimmanci ga nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Buni, wanda tsohon Shugaban APC na ƙasa ne, ya ce haɗin kai da ci gaban jam’iyyar mai mulki na da muhimmanci sosai a gare shi.
Ya kuma bayyana cewa yana da yaƙinin masu neman muƙaman gwamnati a jihar suna da burin yi wa al’umma hidima da inganta rayuwar jama’a.
Ya tabbatar wa ’ya’yan jam’iyyar cewa za a yi tafiyar tare da kowa tare ba tare da la’akari da wanda ya zama ɗan takarar APC ba.
Buni ya kuma yi kira ga ’ya’yan APC a faɗin jihar da su ci gaba da haɗin kai tare da ƙara tallafa wa jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.