Masarautar Dutse ta hukunta wasu dagatai guda 2 bisa zarginsu da laifin barnatar da dukiyar gwamnati
Sarkin Dutse, Mai Martaba Dr. Hameem Nuhu Sunusi ya dakatar da dagacin Kadangare dake karamar hukumar Birnin kudu da kuma korar dagacin unguwar Lautai a karamar hukumar Kiyawa bisa zargin aikata laifuka da suka shafi barnatar da dukiyar gwamnati da sabawa dokokin masarauta.
An dakatar da Ibrahim Adamu, dagacin Kadangare, ne bayan da ya bari aka gudanar da bikin Dodo a filin masarauta, yayin da Amadu Iliya daga Lautai ya rasa mukaminsa saboda bada filin gwamnati haya da karɓar kuɗaɗen da ba a amince da su ba.
Masarautar ta bayyana cewa za ta ci gaba da ɗaukar mataki kan duk wani shugaba na gargajiya da ya kauce wa gaskiya ko ya yi abin da zai bata suna da kima na masarauta.
Sarkin ya sake jaddada cewa masarauta ba za ta lamunci duk wani abu da zai zubar da kimarta ba.