APC Ta Sahale Wa Sanata Goje Neman Takara

0 15

Tsohon gwamnan Jihar Gombe kuma Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Sanata Muhammad Danjuma Goje, ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fafatawa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.

Goje ya bayyana hakan ne bayan kammala tantancewar da jam’iyyar ta gudanar a Abuja, inda kwamitin tantancewa ya amince da shi tare da sauran masu neman takara.

Ya ce har yanzu yana nan daram cikin APC a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa jam’iyyar, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da kare muradun al’ummar Gombe ta Tsakiya.

“Ina sake miƙa kaina ga al’ummata domin su sabunta amanar da suka ɗora min,” in ji shi.

Sanatan ya kuma yaba wa al’ummar ƙananan hukumomin Akko da Yamaltu/Deba bisa irin goyon bayan da suke ci gaba da ba shi, yana mai cewa hakan ne ke ƙara masa ƙwarin gwiwa.

Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran za a yi fafatawa mai zafi wajen neman tikitin Sanatan Gombe ta Tsakiya, musamman bayan goyon bayan da Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nuna wa wani ɗan takarar na daban.

Leave a Reply