Gwamnan Sokoto Ya Kaddamar da Gidajen Yan Gudun Hijira

0 235

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da gidaje 100 da aka gina wa ƴan gudun hijira a ƙaramar hukumar Illela.

Baya ga gidajen, an kuma ƙaddamar da cibiyoyin samar da zaman lafiya da magance ibtila’i, tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin kilowatt 50, da kuma aza harsashin ginin wata babbar kasuwar ƙasa da ƙasa ta Illela.

Gwamna Aliyu ya sanar da bayar da tallafin naira 500,000 ga kowane ɗaya daga cikin mazauna gidaje 100 da aka gina wa ƴan gudun hijirar domin su samu jari na fara sabuwar rayuwa.

“Mun gina waɗannan gidaje ne domin samar wa waɗanda suka rasa matsugunansu muhalli mai aminci da dacewa domin su sake gina rayuwarsu. Haka kuma mun kammala shirye-shiryen gina irin waɗannan gidaje a wasu yankunan jihar da matsalar ƴan bindiga ta shafa,” in ji shi.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda ya ƙaddamar da gidajen ya bayyana cewa: “Gwamnan ya yi abin da ya zarce tsammaninmu. A gaskiya yana ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi nuna ƙwazo a Najeriya. Bayan zaɓensa, ba mu yi tunanin zai kai wannan matakin na aiki ba.”

Shiri da gwamnatin jihar ta aiwatar haɗin gwiwa ne da Hukumar Raya Ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP).

Leave a Reply