Ɗaya Daga Cikin Maniyyatan Najeriya Ta Rasu A Saudiyya

0 17

Hukumar Alhazan Najeriya ta sanar da rasuwar Mallama Aishatu Muhammadu, ɗaya daga cikin maniyyata hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun mataimakiyar daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara, ta ce marigayiyar wadda ta fito daga ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa ta rasu ne sakamakon bugawar zuciya.

Ta rasu ne a yau Lahadi, a kan hanyarsu ta zuwa Madinah daga Jeddah..

NAHCON ta ce shugaban hukumar Ambasada Ismail Abba Yusuf ya tattauna da ɗan’uwan marigayiyar ta waya Umar Jauro Koko, inda aka sanar da iyalanta rasuwarta da fatan Allah ya jiƙanta.

Hukumar ta ce Malama Aisha ta rasu ta bar ƴaƴa da jikoki da dama, cikinsu har da Abdullahi Bello, Babban Baturen Ofishin hukumar sibil difens da ke yankin Ganye.

Leave a Reply