Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Nairobi na ƙasar Kenya domin halartar taron haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da Faransa.
Taron, wanda ake gudanarwa ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar France Emmanuel Macron da shugaban Kenya William Ruto, zai tattauna kan hanyoyin bunƙasa ci gaban tattalin arziki da haɗin gwiwa tsakanin Afirka da Turai.
Rahotanni sun bayyana cewa taron zai fi mayar da hankali kan batutuwan da suka haɗa da makamashi, fasaha, bunƙasa masana’antu, sauyin yanayi da kuma samar da sabbin damammaki ga matasa a nahiyar Afirka.
Ana sa ran shugabannin ƙasashe da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban za su halarci taron domin tattauna hanyoyin ƙarfafa zuba jari da samar da ci gaba mai ɗorewa a nahiyar.
Ziyarar ta Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijeriya ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙa da ƙasashen duniya tare da jawo hannun jarin ƙasashen waje domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.