‎ADC Ta Zargi Tinubu da Kafa Jam’iyyar NDC Domin Raunata Ƴan Adawa

0 101

‎Jam’iyyar adawa ta ADC ta zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC da hannu wajen kafa sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin kan ƴan adawa a Najeriya kafin babban zaɓen shekarar 2027.

‎ADC ta bayyana cewa kafa jam’iyyar NDC wata dabara ce ta siyasa da aka ƙirƙira domin rarraba ƙuri’un masu goyon bayan jam’iyyun hamayya, tare da rage ƙarfin manyan jam’iyyun adawa da ke shirin ƙalubalantar gwamnatin APC mai mulki.

‎Jam’iyyar ta ce maimakon ƙarfafa dimokaraɗiyya, an samar da NDC ne domin kawo cikas ga yunƙurin haɗin kai tsakanin ƴan adawa da kuma rage tasirin su a fagen siyasar ƙasa.

‎Sai dai jam’iyyar APC ta musanta zargin da ADC ke yi, tana mai cewa ba ta da wata alaƙa da kafa jam’iyyar NDC. APC ta bayyana zargin a matsayin mara tushe, tare da cewa jam’iyyar na ci gaba da gudanar da harkokinta bisa tsarin dimokaraɗiyya.

‎Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa da haɗa kawance tsakanin jam’iyyun adawa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Leave a Reply