A wani yunkuri na samar da ruwan sha mai tsafta, gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kashe naira miliyan 292 domin gina sabbin bututun samar da ruwan sha guda 19 da ke amfani da hasken rana.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Hon. Sagir Musa, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin burin gwamnatin jihar na raya abubuwan more rayuwa ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta.
Ya kara da cewa tsarin zai taimaka wajen cike gibin da ake fuskanta na karancin ruwa musamman a karkara, tare da kare muhalli.
A lokaci guda kuma, gwamnati ta sauya sunan ma’aikatar ayyuka ta musamman zuwa Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Ayyuka na Musamman domin fuskantar kalubalen jin kai da ke karuwa a fadin jihar.