Hukumar INEC ta gano kura-kurai a cikin sabbin Jam’iyyun da ta karba guda 110

0 83

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa, INEC, ta bayyana cewa ta karɓi buƙatun rijistar sabbin jam’iyyu 110, amma ta ce ta gano kura-kurai masu yawa a cikin su.

Cikin sabbin jam’iyyun da ake neman rijista akwai waɗanda ke da goyon bayan fitattun ’yan siyasa kamar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, da Peter Obi, sai dai wasu suna da sunaye da alamu masu kama da juna.

Wasu daga cikin takardun sun rasa muhimmancin bayani irin su sunayen shugabanni, adireshi ko tambarin jam’iyya, har ma da wadanda suka gabatar da buƙatu biyu da shugabanci daban-daban.

Hukumar ta INEC ta ce za ta bi ƙa’idojin doka cikin bin diddigin waɗannan buƙatu yayin da ake shirin yin zaben gwamnan Anambra a watan Nuwamba.

Leave a Reply