Shugaban kasa Bola Tinubu zai sanya hannu a yau Alhamis kan sabbin dokoki huɗu da za su canza tsarin haraji da tattara kudaden shiga a fadin kasar nan.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa dokokin sun samu amincewar majalisa bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kuma ana sa ran za su haɓaka tara haraji da jawo jarin cikin gida da waje.
Daga cikin dokokin akwai kafa sabuwar hukumar tara haraji mai cin gashin kanta, da samar da tsarin aiki guda da kuma hukumar haɗin gwiwar hukumomin tara haraji daga matakin ƙasa har zuwa ƙananan hukumomi.
Manyan jami’an gwamnati da shugabannin majalisa da gwamnonin jihohi za su halarci bikin sanya hannu, abin da ke nuna muhimmancin wadannan dokoki.