Hukumar yan sanda ta kasa ta zata hada hannu da kwamatin kasa da kasa na hukumar agaji ta Red Cross da sauran hukumomin cigaba, wajen bayar da horo ga sabuwar rundunar SWAT da ta maye gurbin rundunar yan sanda ta musamman dake yaki da ayyukan fashi da makami wato SARS.
Kusan jami’ai 1,850 ne ake sa ran zasu halarci shirin bayar da horon na tsawon makonni 3, wanda za’a gudanar a makarantar baiwa yan sanda horo dake Ila Oragun a jihar Osun, da kuma ta Ende Hills dake jihar Nassarawa.
Kakakin hukumar Frank Mba, yace jami’an sabuwar rundunar ta SWAT, zasu karbi horo ne kan dokokin kiyaye dan adam da hakkokinsa, makamar jami’in dan sanda a halin rikici, kamawa da kuma tsare mai laifi da dai makamantansu.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Masu gudanar da shirin bada horon sun hadar da jami’ai daga hukumomin cigaba, kwararru a fannin tsaro da kuma yan fafutuka daga kungiyoyn fararen hula.