’Yan Najeriya Miliyan 34.7 Na Fuskantar Barazanar Yunwa — MDD

Aƙalla ’yan Najeriya miliyan 34.7, ciki har da ’yan gudun hijira miliyan 1.4 da ke zaune a Arewa maso Gabas, na fuskantar barazanar matsanancin yunwa, a cewar wani rahoto daga Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Rahoton wanda ofishin kula da agaji na MDD (UNOCHA), tare da haɗin gwiwar hukumar kula da abinci ta duniya (FAO) da gwamnatin Najeriya suka fitar, ya bayyana cewa daga watan Yuni zuwa Agusta 2025, mutane miliyan 33.1 ake sa ran za su fuskanci karancin abinci mai tsanani.

Rahoton ya nuna cewa yunwar ta fi kamari a jihohin Adamawa, Borno, da Yobe, inda yara kusan miliyan 1.8 ke fama da matsanancin karancin abinci.

Majalisar ta danganta wannan matsala da hauhawar farashin kayayyaki da ya kai kashi 40.9 cikin dari a watan Yuni 2024, da kuma raguwa ko katsewar tallafin agaji daga ƙasashen waje, musamman daga Amurka.

Comments (0)
Add Comment