‘Yan Sanda Sun Kama Masu Damfara Da Jabun Dala A Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin damfarar wani mutum daga jihar Kano ta amfani da jabun kudin dalar Amurka a yankin Shuwarin.

Jami’an rundunar sun samu nasarar kama wadanda ake zargin tare da kwato guda 35 na jabun kudin dalar Amurka (USD) da ake zargin sun yi amfani da su wajen aikata laifin.

Rundunar ta ce bincike ya fara domin gano yadda aka samu kudaden da kuma ko akwai wasu da ke da hannu a lamarin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Jigawa, Haruna A. Yahaya, ya gargadi al’umma da su guji mu’amala da duk wata hanya ta damfara ko kudaden bogi, tare da bukatar jama’a su rika bai wa jami’an tsaro bayanan sirri domin dakile irin wadannan laifuffuka.

Comments (0)
Add Comment