Yansanda sun kama wani fasto kan zargin lakaɗawa yara duka a jihar Ribas

Rundunar ƴansanda a jihar Ribas ta kama wani fasto da wasu ma’aikatansa biyu a jihar Ribas, kan zargin lakaɗawa yara duka lokacin wani taro da aka kwatanta da “taron tsarkakewa”.

Jami’in ƴansanda na yankin Eneka a jihar, Akpo Lewis, shi ya tabbatar da kama faston da wasu ma’aikatan cocin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna malaman cocin na mai suna Ifediorah Joseph, na lakaɗawa yaran waɗanda ba su haura shekaru biyar zuwa tara ba duka ta hanyar amfani da iccen kwakwa lokacin bikin.

Har ila yau, ana iya ganin yadda faston ya yi ta dukan yaran sau da dama, kafin ya miƙa su hannun wani mamba a cocin, wanda shi kuma ya aika su ga wata ƙungiya da ake wa lakabi da “ƙungiyar tsarkakewa”.

Sauran waɗanda aka kaman sun haɗa da sakataren walwala na cocin, Promise Nwikegha da kuma wata mai addu’a Deborah Ohia.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa a idon iyaye aka lakaɗawa yaransu duka kuma sun ce suna da matsaniya kan bikin.

Comments (0)
Add Comment