Ɗan Takarar Gwamnan ADC A Gombe Ya Fice Daga Jam’iyyar

Ɗan takarar Gwamnan ADC a Gombe ya fice daga jam’iyyar

Ɗaya daga cikin ’yan takarar kujerar Gwamnan Jihar Gombe da suka fafata a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ADC, Injiniya Adamu Mohammed Maaji, ya fice daga jam’iyyar.

Maaji ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 10 ga Agusta, 2026, wadda ya aika wa Shugaban ADC na Jihar Gombe ta hannun shugabannin jam’iyyar na mazaɓar Wange da ke Karamar Hukumar Kaltungo.

A cikin wasiƙar mai taken “Ficewa daga ADC”, Maaji ya ce ya yanke shawarar janyewa daga kasancewa ɗan jam’iyyar nan take.

Ya ce, “Ina sanar da ku shawarar da na yanke ta janyewa daga kasancewa ɗan jam’iyyar ADC nan take.”

Tsohon ɗan takarar gwamnan ya gode wa jami’an jam’iyyar tun daga matakin mazaɓa zuwa jiha bisa damar da suka ba shi na damawa a harkokin siyasa.

Ya ce kasancewarsa cikin jam’iyyar ya ba shi damar samun sababbin abokai tare da ƙara ƙwarewa a harkokin siyasa.

Maaji ya ce, “Ina gode wa jami’an jam’iyyar tun daga mazaba zuwa matakin jiha bisa damar da suka ba ni na samun sababbin abokai da kuma gina ƙwarewa a harkokin siyasa.”

Sai dai Maaji bai bayyana dalilin da ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar ba, amma ya yi mata fatan samun nasara a harkokinta na gaba.

Murabus ɗin Maaji na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a Jihar Gombe gabanin babban Zaɓen 2027, inda ’yan siyasa da masu neman takara daga jam’iyyu daban-daban ke ƙulla sabbin dabaru domin ƙarfafa matsayinsu na siyasa.

Comments (0)
Add Comment