An Kama Tsohon Ciyaman Kan Zargin Sayar da Miyagun Kwayoyi A Kano

An kama tsohon ciyaman kan zargin sayar da miyagun ƙwayoyi a Kano

An kama wani tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Rogo bisa zargin sayarwa da yi wa matasa allurar Fentanyl, wata ƙwaya mai matuƙar haɗari.

Shugaban kwamitin haɗin gwiwa na hukumomi da dama kan yaƙi da haramtattun ƙwayoyi da laifukan da suka shafe su na Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ne ya bayyana kamen a wata hira ta bidiyo da wasu maname labarai a ranar Litinin.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wani binciken sirri da jami’an kwamitin suka gudanar ya tabbatar da zargin cewa yana samar da ƙwayar ga matasa.

Sai dai Rimingado bai bayyana sunan tsohon shugaban ƙaramar hukumar ba.

Ya bayyana cewa binciken ya samo asali ne bayan kwamitin ya kama wani matashi wanda hannunsa ya lalace matuƙa sakamakon yawan yi masa allurar ƙwayar.

A cewarsa, daga baya matashin ya bayyana wa masu binciken cewa tsohon shugaban ƙaramar hukumar ne yake samo masa ƙwayoyin.

Rimingado ya ce jami’an kwamitin sun bi sawun matashin har zuwa wajen wanda ake zargin, inda ya ba shi kuɗi sannan ya ce ya dawo daga baya.

Ya ce lokacin da matashin ya dawo, wanda ake zargin ya ɓoye ƙwayar a cikin wata ambulan yana shirin miƙa masa, sai jami’an kwamitin suka shiga suka kama shi.

Ya ce, “Da farko wanda ake zargin ya musanta cewa yana da hannu kai tsaye, sai dai ya bayyana cewa ana kawo ƙwayoyin ne daga Kasuwar Sabon Gari.”

Sai dai kwamitin ya ce ya samu isassun hujjoji da suka haɗa da ƙwayar da aka samu a hannunsa, bayanan matashin da kuma bayanin da wanda ake zargin da kansa ya bayar.

Kwamitin ya kuma bayyana cewa an rufe cibiyar lafiya da wanda ake zargin ke gudanarwa bayan hukumomi sun tabbatar da cewa ba ta da cikakken lasisi.

Rimingado ya zargi tsohon ciyaman ɗin da yin aikin jinya ba tare da ingantacciyar lasisin jinya ba tun daga shekarar 1985, tare da zargin cewa ya taɓa gudanar da ayyukan karɓar haihuwa ta hanyar tiyata duk da rashin cancantar yin hakan.

A cewar Rimingado, an gurfanar da wanda ake zargin bisa Sashe na 249 na Dokar Penal Code ta Kano, wanda ke da nasaba da laifukan da suka shafi yi wa mutum amfani da abubuwa masu cutarwa.

Ya jaddada cewa kwamitin zai gabatar da ƙwararan hujjoji a gaban kotu.

Rahotanni sun ce matashin ya shaida wa masu bincike cewa ya kashe sama da Naira miliyan biyu wajen sayen allurar cikin shekaru biyu.

Rimingado ya bayyana wannan lamari a matsayin abin damuwa, yana mai cewa yana nuna irin tsananin matsalar shaye-shayen ƙwayoyi a jihar.

Comments (0)
Add Comment