Da ni Tinubu ya tura Osun, da mun kayar da Adeleke – Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce da Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da cikakken ƙarfin gwamnatin tarayya wajen ganin APC ta lashe zaɓen gwamnan Osun, da ya je jihar da kansa domin taimakawa wajen kayar da Gwamna Ademola Adeleke.
Wike ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da tasirinta wajen ƙwaace zaɓen domin APC ta yi nasara ba.
Ya ce da Tinubu ya so APC ta lashe zaɓen ko ta halin ƙaƙa, da shi ma zai je Osun, kuma da an ga bambancin sakamako.
Ya bayyana haka ne ranar Talata bayan ya kammala duba wasu wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a Maitama, Abuja.
Wike ya kuma ce ya kamata a ce Adeleke yana cikin APC ne da abubuwa sun tafi yadda ya kamata.
A zaɓen da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, INEC ta bayyana Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya lashe ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30, yayin da ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya lashe 11.