Malaman da suka ajiye aiki a jami’ar KASU ba su wuce 50 ba – Gwamnatin Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ƙarin bayani kan turka-turkar da ake yi tsakaninta da malaman Jami’ar Jihar, KASU, bayan da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi iƙirarin cewa sama da malamai 200 sun ajiye aikinsu saboda rashin kyawawan yanayin aiki.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya shaida wa BBC cewa rahotannin da ASUU ke yaɗawa ba gaskiya ba ne.
Ya ce gwamnatin jihar ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen biyan da dama daga cikin buƙatun malaman cikin sama da shekaru ukun da ta yi tana mulki.
Ya ce yawan waɗanda ake cewa sun ajiye aiki bai wuce mutum 50 ba cikin shekaru ukun da gwamnatin ta yi, kuma mafi yawansu sun samu sauyin wurin aiki ne, ba wai saboda rashin jin daɗin yanayin aiki ba.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati na tattaunawa da malaman jami’ar domin lalubo mafita kan matsalolin da suka taso.
Ita ma jami’ar ta KASU ta musanta iƙirarin ASUU, inda ta ce rahoton cewa malamai sama da 200 sun yi murabus ba ya cikin bayanan jami’ar.
Shugaban jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, a wata sanarwa da ya fitar ya ƙalubalanci ASUU da ta gabatar da hujjoji da sunayen waɗanda ake zargin sun yi murabus, kwanakin da suka yi murabus da kuma dalilan da suka sa suka bar Jami’ar Jihar Kaduna.