A wani labarin kuma, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya tana tantance kamfanonin cikin gida 19 domin samar da maganin gargajiyan da zai magance cutar corona.
Kamfanonin sun yi ikirari daban-daban, wadanda suka hada da samar da maganin cutar corona kai tsaye zuwa samar da maganin da zai warkar da alamun cutar.
Kamfanonin sun gana da shugabannin ma’aikatar tare da sashen kula da magungunan gargajiya.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Sai dai, an bukaci kamfanonin da su gabatar da samfurin magungunansu zuwa ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, daga cikinsu za a zabi kamfanoni 3 wadanda za a tallafawa da kudade.
Karamin ministan lafiya, Sanata Adeleke Mamora, shine ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai.