Gwamna Badaru ya yabawa babban sufeton ‘yansanda bisa kokarin sa na samar da zaman lafiya

Gwamnatin jihar Jigawa ta yabawa babban sufetan ‘yan sanda na kasa bisa kokarinsa na samar da zaman lafiya da kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin babban sufetan ‘yan sanda na kasa Usman Alkali Baba a gidan gwamnati dake Dutse.

Yace ya zama wajibi a yabawa babban sufetan bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen bullo da tsare tsaren kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.

Gwamna Badaru ya bayar da tabbacin cigaba da hada kai da yansanda da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma.

A jawabinsa babban sufetan yansandan na kasa Usman Baba Alkali yace sun kawo ziyara jihar Jigawa ne a cigaba da rangadin jihoshin kasarnan 36.

Ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa hadin kai da tallafin da take bawa hukumomin tsaro.

Comments (0)
Add Comment