Gwamnatin Gombe ta ware N260m don sauya wa kasuwar hatsi matsuguni
Gwamnatin Jihar Gombe, ta amince da ware Naira miliyan 200 domin samar da abubuwan more rayuwa da ake buƙata wajen sauya wa Kasuwar Hatsi ta Gombe zuwa yankin titin Dukku.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Moses Kyari-Bolda ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai.
Ya ce Ƙaramar Hukumar Gombe ta kuma ware ƙarin Naira miliyan 60 domin tallafa wa aikin, wanda ya kai jimillar kuɗin da aka ware Naira miliyan 260.
Kwamishinan, ya ce wani ɓangare na kuɗin zai kasance na biyan diyya ga mutanen da sauyin matsugunin kasuwar zai shafa.
Ya bayyana cewa mayar da kasuwar zuwa titin Dukku zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa tare da inganta harkokin kasuwanci.
A cewarsa, sabon wajen zai kasance da tsari mai kyau, wanda zai bai wa ’yan kasuwa damar gudanar da harkokinsu cikin sauƙi.
Ya kuma ce matakin zai taimaka wajen kare wani tsohuwar masallaci mai tarihi da gwamnatin jihar ke shirin adanawa a matsayin abin tarihi.
Kyari-Bolda, ya ce mayar da kasuwar na daga cikin shirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na inganta tsarin birane, samar da ababen more rayuwa da bunƙasa kasuwanci.
Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar jihar tare da amfani da dukiyar jama’a yadda ya kamata.