TUC za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin Jigawa don walwalar ma’aikata
Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC reshen Jihar Jigawa, ta yaba wa Gwamna Umar Namadi, kan yadda gwamnatinsa ke kula da jin daɗin ma’aikata a jihar.
Ƙungiyar ta kuma ce za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin jihar domin samun ci gaba.
Shugabannin TUC sun bayyana hakan ne a lokacin da suka da suka kai wa Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Bala Ibrahim, inda suka kuma gabatar masa da sabon shugabancin ƙungiyar na jihar.
Shugaban TUC na Jigawa, Ali Sa’adu Dutse, ya yaba wa Gwamna Namadi kan ayyukan raya jihar da gwamnatinsa ta gudanar tun bayan da ya zama gwamna a shekarar 2023.
Ya ce gwamnatin ta aiwatar da ayyuka a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, samar da ababen more rayuwa, tallafa wa matasa da kuma walwalar ma’aikata.
Ya ƙara da cewa biyan albashi, fansho da sauran haƙƙoƙin ma’aikata a kan lokaci ya ƙara ƙarfafa amincewar ma’aikata da gwamnatin jihar.
A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin jihar, Bala Ibrahim, ya gode wa shugabannin TUC kan ziyarar.
Ya ce gwamnatin Namadi ta inganta tsarin fansho tare da tabbatar da biyan albashi da fansho a kai a kai.
Ya kuma ce gwamnatin ta aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar.
Bala Ibrahim, ya tabbatar wa ƙungiyar TUC cewa gwamnati za ta ci gaba da yin aiki tare da ƙungiyoyin ƙwadago domin kare haƙƙoƙin ma’aikata da samun ci gaba a jihar.
Ya kuma buƙaci ma’aikata su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da sadaukarwa.
“Za mu ci gaba da kasancewa tare da ku. Tare za mu gina Jigawa mai cike da wadata,” in ji shi.