Mutum 3,000 Sun Yi Hijira Saboda Hare-Haren ’Yan Bindiga A Katsina

Mutum 3,000 sun yi hijira saboda hare-haren ’yan bindiga a Katsina

Sama da mutum 3,000 mazauna Unguwar Guru da ke Ƙaramar Hukumar Kankia a Jihar Katsina ne, suka bar gidajensu sakamakon yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

A yanzu haka, mutanen sun nemi mafaka a gine-ginen da ba a kammala ba, makarantar firamare da kuma gidajen ’yan uwansu a wasu garuruwa.

Sabbin hare-haren sun faru ne ranar Asabar da Litinin, inda aka kashe mutane 13 tare da sace wasu mata da ’yan mata.

Mazauna yankin da suka shafe sama da kwanaki tara a garin Rimaye, sun ce sun bar gidajensu ba tare da sun ɗauki komai ba.

Sun kuma ce har yanzu ba su samu wani tallafi daga gwamnatin jihar ko ta tarayya ba.

Wani mazaunin yankin, Muhammadu Lurwanu, ya ce kusan dukkanin mazauna Unguwar Guru sun tsere.

Ya roki gwamnati ta samar musu da abinci, ruwa, tufafi da sauran kayan agaji.

Wani mazaunin yankin, Muhammadu Sagiru, ya ce hare-haren sun jefa mutane cikin firgici da damuwa.

Ya ce an kashe kusan mutane takwas, yayin da aƙalla mutane biyar, ciki har da shi, suka samu rauni.

Mazauna yankin sun kuma ce an ƙone wasu gidaje, yayin da mutane da dama suka rabu iyalansu kuma ba su san inda wasu daga cikin ’yan uwansu suke ba.

Sun bayyana damuwa cewa har yanzu ’yan bindigar na zaune a yankin, tare da neman ƙarin jami’an tsaro domin su samu damar komawa su kwashe amfanin gonakinsu.

Sun kuma buƙaci gwamnati ta samar musu da abinci, ruwa mai tsafta, banɗakuna da sauran kayan more rayuwa, tare da gargaɗin cewa rashin tsafta na iya haifar da ɓarkewar cututtuka, musamman tsakanin yara.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce tana jiran cikakken rahoto daga hukumomin yankin kafin ta yanke shawarar matakin da ya dace.

Gwamnatin ta ce ta fahimci halin da mutanen da suka rasa matsugunansu ke ciki, tare da gode wa al’ummomin da suka ba su mafaka.

Comments (0)
Add Comment