Hukumar NCDC ta sanar da sabbin mutane 573 da suka harbu da cutar Corona

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta sanar da sabbin mutane 573 da suka harbu da cutar Corona a kasa baki daya.

NCDC ta sanar da cewa mutanen sun fito ne daga Jihohi 7 na kasar nan.

Cibiyar ta ce Lagos (281), Benue (202), Kano (61), Borno (20), Jigawa (5), Edo (2), and Oyo (2)

NCDC ta kuma ce mutane 572 ne aka sallame su a jiya daga cibiyoyin kula da masu cutar, wanda hakan ya ke nuni da cewa kimanin mutane dubu 215 da 39 ne suka warke daga cutar a kasa baki daya.

Haka kuma an bada rahotan cewa Mutane 3 ne cutar Corona ta hallaka a jiya wanda hakan ya kawo adadin mutanen da cutar ta kashe zuwa dubu 3 da 39.

Kazalika, an bada rahotan cewa kimanin mutane dubu 243 da 450 ne suka harbu da cutar tun bayan bayyanarta a jihohi 36 ciki harda birnin tarayya Abuja.

Comments (0)
Add Comment