Jagoran addinin Iran Ya Yi wa Amurka Hannunka Mai-sanda

Jagoran addinin Islama na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya gargadi Amurka cewa ba za a samu sassauci daga Tehran ba kan shirinta na makamin mai linzami muddin Amurka na goce wa Isra’ila da tsoma baki a Gabas ta Tsakiya.

Khamenei ya bayyana hakan ne yayin wani taron dalibai a Tehran, a bikin cika shekaru 46 da mamaye ofishin jakadancin Amurka a 1979, wanda ke daya daga cikin manyan lokuta da suka girgiza tarihin Iran.

Ya ce: “Za mu iya yin hulɗa da Amurka ne kawai idan ta daina goyon bayan Isra’ila, ta kuma janye dakarunta daga yankin Gabas ta Tsakiya”.

Kalaman Khamenei sun zo ne bayan yakin kwanaki 12 da ya barke a watan Yuni, sakamakon hare-haren Isra’ila kan Iran, abin da ya jawo Amurka ta kai farmaki kan wasu wuraren nukiliya na kasar. Wannan ya hana ci gaba da tattaunawar nukiliya da ake yi tsakanin kasashen biyu.

Iran ta dade tana fama da takunkuman tattalin arziki daga kasashen Yammacin Duniya, musamman bayan Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliya a 2018.

A watan Satumba 2025, Majalisar Dinkin Duniya ta sake farfado da wasu daga cikin takunkuman bayan Birtaniya, Faransa da Jamus sun nemi hakan.

A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce Tehran na shirye ta koma teburin tattaunawa da Amurka amma kan batun makamashin nukiliya kawai, ba kan makamai masu linzami ba.

Comments (0)
Add Comment