Kotun Kwadago Ta Ƙasa da Ke Zamanta A Abuja, Ta Umarci Ma’aikatan FCTA Da Su Dakatar da Yajin Aiki

Kotun Kwadago ta Ƙasa da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi,wanda ke tilasta wa ma’aikatan FCTA ƙarƙashin Joint Union Action Committee su dakatar da yajin aikin da suke yi.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tare da Hukumar FCTA ne suka shigar da ƙarar suna neman da a hana shugabannin ƙungiyar kiran duk wani yajin aiki ko tsayuwar aiki.

An shigar da ƙarar ne a gaban Kotun Kwadago da ke Abuja, inda aka tuhumi shugabar JUAC, Rifkatu Iortyer, da sakatarenta Abdullahi Umar Saleh.

Alƙalin ya bayyana cewa da zarar an kai rikici gaban Kotun Kwadago, dole ne a dakatar da duk wani yajin aiki har sai an kammala shari’ar.

Kotun ta bayar da umarnin hana ci gaba da yajin aikin, inda ta ce umarnin zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a yanke hukunci na ƙarshe.

An ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Maris, 2026, domin sauraron cikakken karar.

Comments (0)
Add Comment