Rundunar ‘yansandan jihar Kano tace ta kama wani mutum bisa zargin yiwa mata sama da 40 fyade a jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna ya rabawa manema labarai a Kano.
Yace yansanda sun kama Muhammad Alfa mai shekaru 32 a duniya a Kwanar Dangora, kusa da birnin Kano.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Ya kara da cewa yayin bincike, mutumin ya furta cewa ya yiwa sama da mata 40 fyade a shekara guda, cikinsu har da yara, da matan aure, har da wata tsohuwar ‘yar shekaru 80.
A cewarsa, an kama mai laifin lokacin da yake kokarin yiwa wata matar aure fyade a gidanta.
Abdullahi Haruna yace jama’a sun yi farin ciki bayan samun labarin cewa ‘yansanda sun kama mutumin.