Matashin da Ya Yiwa Mata 40 Fyade Ya Shiga Hannu a Kano

0 105

Rundunar ‘yansandan jihar Kano tace ta kama wani mutum bisa zargin yiwa mata sama da 40 fyade a jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna ya rabawa manema labarai a Kano.

Yace yansanda sun kama Muhammad Alfa mai shekaru 32 a duniya a Kwanar Dangora, kusa da birnin Kano.

Ya kara da cewa yayin bincike, mutumin ya furta cewa ya yiwa sama da mata 40 fyade a shekara guda, cikinsu har da yara, da matan aure, har da wata tsohuwar ‘yar shekaru 80.

A cewarsa, an kama mai laifin lokacin da yake kokarin yiwa wata matar aure fyade a gidanta.

Abdullahi Haruna yace jama’a sun yi farin ciki bayan samun labarin cewa ‘yansanda sun kama mutumin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: