Dabarun yin rubutu mai ma’ana a kafar yada labarun Zamani (social media)

0 132

Babu yadda za’ai aikin mai ilimi yayi dai-dai da na wanda ba shi da masaniya.

Bayan dogon nazari da nayi kan yadda yawancin mutane suke amfani da kafafen sadarwa na zamani (social media) na iya gano kurakurai da bankaurar da masu amfani da fagen ke yi.

Hakan ta sanya yau na zabi yin dan tsokaci kan wannan batun domin watakil wasu zasu fahimta har ma suyi aiki da shawara ta don inganta rubutunsu a dandalin, watakil ma abinda suke rubutawa ya amfani mai karantawa kuma sakon ya je ga wanda akai niyya.

Zabar batu (Topic)

Da farko dai kada ya zama kai komai ka gani sai kayi magana akai kamar wani karan da dare ya yiwa a juji. Ya kamata a ce kana da zabin abubuwan da zaka fi mayar da hankali a kai. Kamar siyasa, tsaro, da ilimi ko kuma addini.

Yanzu mu kaddara ka zabi abinda kake son yin magana akai, to amma wacce hanya zaka bi don yin rubutu mai ma’ana dake kunshe da sako kai tsaye kuma mai jan hankali ga mutane?

Matakin farko

Me ka sani game da abinda kake son yin magana akai?

Ko kawai a social media ka gani amma ka nace sai kayi magana? Hanya mafi dacewa shi ne ka yi bincike akan komai, ka san inda aka fara da inda ke yanzu da kuma inda ake shirin zuwa. Idan ba haka ba kuma wata rana za’a yi faduwar bakar tasa.

Shinfida da sanya komai a muhallinsa (Background)

Wasu mutane kan zabi su dauki maganar wasu ba tare da tantancewa ba, ba su san daga inda wancan ya samo maganar ba, kuma dadin nuna jahilcinsu shi ne, sai su boye sunan wanda suka dauko maganar a wurinsa domin masu karatu su tsammaci su ne suka yi da kansu.

Matukar rubutu mai ma’ana kake son yi to lallai ka fadi wanda yayi magana ko wurin da ka dauko ta. Kuma a farko kafin kayi nisa cikin rubutunka yana da kyau ka yi karamin jawabi kan ainihin maudu’in da zaka yi magana akai. Malam Muhsin da Idris Hamza Yana suna amfani da wannan salon.

A cikin rubutunka, kabi irin salon rubutun Dr. Maude Gwadabe na yin rubutu kadai idan kana da masaniya akan batun kuma ba ko yaushe ba sai jifa-jifa.

Haka zalika, idan ka yi shinfida, ka kuma fadi matsalar, kada ka gaza bayyana matsayinka akan batun da kake jawabi akai. Goyon baya kake ko kuma suka kake? Yana da alfanu ka bayyana inda ka dosa.

Sirrin rubutu mai ma’ana

Bayan wannan, mafi tasiri shi ne ka sa a ranka cewa ba babatu kake yi ba. Zaka cimma haka ne idan a karshen rubutunka ka bayar da shawara ko mafita kan batun da kake magana akai, kada kayi soki burutsu kawai ka wuce.

Kada ka zama kamar mahaukacin kare da komai ya gani zai yi ta yin haushi a Social Media babu dalili, ka tabbatar abinda ka rubuta zai amfane ka ko waninka.

Ka tuna duk abinda harshenka ya furta da abinda hannuwaka suka aikata ciki har da rubutu zai zama hujja gare ka ko kuma akanka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: