Ƙungiyar makarantun islamiyya a jihar Kano sun bayyana ƙorafinsu akan yadda gwamnatin jihar Kano ta buɗe gidajen kallon bal a faɗin jihar inda kuma ta bar makarantun islamiyya a garƙame.
Wannan ƙorafi ya fito ne daga bakin wasu daga cikin shugabannin Islamiyya Aisha Ibrahim Ɗorayi da kuma Malam Hassan, a lokacin da su ke tattunawa da filin inda ranka da ake gabatarwa a tashar Freedom Radio da ke Kano.
Malaman makarantun Islamiyya sun ce za su yi zanga-zangar lumana ganin yadda gwamnati ta bude gidan kallo amma bata bude makarantun Islamiyya ba.
- Gwamnatin Sokoto Ta Bai Wa Sojojin Najeriya Gudummuwar Motocin Sulke 62
- Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina
- Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana
- EFCC Ta Gurfanar da Bello Bodejo Kan Zargin Badaƙalar Kuɗi
- Ma’aikatan Abuja Ba Sa Sona — Wike
Wannan dai yana zuwa ne kwanaki uku da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin buɗe gidajen kallon ball da ke jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gidajen kallo a jihar Kano.
Hakazalika gwamnan ya yi kira ga masu gidan kallon su tabbatar da cewa an baiwa juna tazara a gidajen kallonsu.
A ƙarshe gwamna Ganduje ya ba su gudunmuwar takunkumin rufe baki guda 40,000 saboda suyi amfani da su wajen kalle-kallensu.