Hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya ta ayyana cewa annobar corona zata iya jawo asarar guraben ayyukan yi miliyan 13 a Najeriya.
A cewar hukumar, Najeriya na bukatar agajin gaggawa na kudade domin bunkasa tattalin arzikin kasar, kasancewar miliyoyin yan kasarnan a halin yanzu suna fuskantar mummunar illar da kwayar cutar ta yiwa tattalin arziki.
- Jagoran juyin mulkin Gabon na yin kokarin kawo karshen takunkumin da aka kakabawa kasar
- Rikicin soyayya ya yi sandiyyar mutuwar wani matashi dan jami’a
- An kama wasu mutane 2 bisa zargin kisan wani mutum a jihar Filato
- Gwamnatin Najeriya na kokarin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya
- Ana tuhumar mai dakin Ali Bongo da laifin karkatar da kudade da wasu laifuffuka
Babbar mai magana da yawun bakin hukumar, Elisabeth Baris ta fada cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar cewa ana bukatar kudi sama da dala Miliyan 182 domin cigaban ayyukan ceton rayuwa a kasarnan wacce tafi kowacce yawan mutane a nahiyar Afirka, cikin watannin 6 masu zuwa.
Ta bayyana cewa sama da ‘yan kasarnan miliyan 3 da dubu 800, musamman masu kananan sana’o’i, zasu iya rasa ayyukan su, inda ta kara da cewa adadin zai iya karuwa zuwa miliyan 13 muddin dokar hana tafiye-tafiye ta cigaba da aiki tsawon lokaci.