Sufeto Janar na Yansanda, Mohammed Adamu, ya dakatar da bukatar cancanta domin wadanda ke neman shiga aikin dansanda a matsayin kurata.
Mohammed Adamu a wani umarni da ya bayar, yace babu wadanda za a hana dama a wajen daukar aikin, bisa la’akari da yanayin halittarsa ko shekarunsa ko matakin karatunsa.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Hukumar a halin yanzu tana aikin daukar kuratan yansanda dubu goma domin magance karancin yansanda, kuma tuni aka fara aikin tantance masu neman aikin daga jiya Litinin zuwa ranar goma sha shida ga watan gobe na Satumba.
Kamar yadda yazo a wata sanarwa da kakakin hukumar dansanda, Frank Mba, ya fitar, ana sa ran masu neman shiga aikin suzo da number shaidar zama dan kasa da takardun karatu na ainihi da kwafi bibiyu, da takardar shaidar zama dan karamar hukuma da ta haihuwa, wadanda aka shirya cikin fararen files guda biyu, tare da kananan hotuna na fasfo.