Shugaban Kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, Zai Ziyarci Kasar Faransa a Yau

Shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, zai ziyarci kasar Faransa a yau domin ganawa da takwaransa Emmanuel Macron a birnin Paris, lamarin da masana ke ganin na iya zama sabon babi a dangantakar ƙasashen biyu, in ji rahoton RFI na Faransa..

Ziyarar na zuwa ne a lokacin da ake ganin akwai wani sabon daidaita alaƙa tsakanin Faransa da Afrika, wanda ya bayyana a Senegal bayan rufe sansanonin sojojin Faransa na ƙarshe kimanin watanni biyu da suka wuce.

A Dakar kuwa, har yanzu akwai tsoffin koke-koke da ake yi wa Faransa ta miƙa bayanan soja da na shari’a kan kisan kiyashin da aka yi a watan Disambar 1944, abin da bai samu mafita ba.

Haka kuma, batutuwan tattalin arziki suna cikin tattaunawar, musamman rikicin bashi na euro miliyan 150 da ya shafi aikin jirgin ƙasa na Dakar–Diamniadio.

Fadar shugaban Faransa ta bayyana cewa shugabannin biyu za su tattauna kan rikice-rikicen yankin da muhimman al’amuran ƙasa da ƙasa, sannan Shugaba Faye zai halarci taron ‘yan kasuwar Faransa da ƙungiyar Medef ta shirya.

Comments (0)
Add Comment