Shugaban Malissar Dinkin Duniya Yace Majalissar Na Fuskantar Matsalar Kudi

Majalisar Dinkin Duniya na cikin hadarin durƙushewa saboda ƙasashe mambobin ƙungiyar ba su biya kuɗaɗensu ba, in ji shugaban majalisar.

António Guterres ya ce Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar matsalar kuɗi wanda ke “kara zurfafa barazanar rashin iya aiwatar da shirye-shirye”, kuma kuɗin da ke asusunta na iya ƙarewa a watan Yuli mai zuwa.

A wata wasiƙa da ya aikewa ɗaukacin ƙasashe mambobi 193, Guterres ya ce dole ne su mutunta alƙawarin biyan kuɗaɗen da suka wajaba ko kuma su yi garambawul ga dokokin kudi na majalisar domin gudun durƙushewa.

Hakan na zuwa ne bayan babbar mai ba da gudummawa ta Majalisar Dinkin Duniya, Amurka, ta ƙi ba da gudummawa a cikin kasafin kudinta na yau da kullun da na wanzar da zaman lafiya, tare da ficewa daga hukumomi da dama da ta kira “barnar dalar masu biyan haraji”.

Ana bin wasu mambobi da dama bashi wasu kuma kawai sun ƙi biyan kuɗaɗen.

Comments (0)
Add Comment