Sojoji a Mali sun maido da iko a sansanoni uku da ke tsakiyar kasar bayan da mayakan jihadi suka kai musu wani hari

Sojoji a Mali sun maido da iko a sansanoni uku da ke tsakiyar kasar bayan da mayakan jihadi suka kai musu hari a lokaci guda.

A cewar sanarwar Sojoji 6 ne suka mutu sannan aka kashe mayakan makiya 11.

An kuma kai wani sabon hari a makwabciyar kasar Burkina Faso.

Wadannan hare-hare guda hudu na masu jihadi sun nuna yadda dakarun soji ke da rauni a yankin Sahel.

A yayin da wasu ‘yan kunar bakin wake ke tuka motoci cike da bama-bamai su tunkari sansanonin sojoji a yankin Mopti na kasar Mali.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da wata kungiyar masu da’awar jihadi take kashe sojoji da fararen hula a kan iyakar Arewacin Burkina Faso.

Kafin hakan dai, sojojin kasashen biyu, sun kwace mulki bayan da suka zargi zababbun gwamnatocin fararen hula da kasa tinkarar masu jihadi.

Comments (0)
Add Comment