Ɗan takarar gwamnan PDP tsagin Turaki a Gombe ya fice daga jam’iyyar
Honarabul Ahmed Mohammad Yayari, ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe, na jam’iyyar PDP tsagin da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta, ya fice daga jam’iyyar.
Yayari, wanda aka fi sani da Sardauan Gona, ya sanar da ficewarsa a wata wasiƙa mai kwanan wata 11 ga watan Agusta 2026, wadda ya aike wa shugaban PDP na mazaɓar Kalshingi a Ƙaramar Hukumar Akko.
A wasiƙar, Yayari ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne bayan dogon nazari da tuntuɓar iyalansa, abokansa, shugabannin al’umma, da kuma magoya bayansa.
Sai dai bai bayyana dalilin da ya sa ya fice jam’iyyar ba, kuma bai bayyana jam’iyyar ko tafiyar siyasar da zai bi ba.
Yayari ya gode wa shugabannin PDP da mambobin jam’iyyar bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake cikinta.
Ya kuma buƙaci a cire sunansa daga kundin mambobin PDP na mazaɓar Kalshingi.
Shugaban PDP na mazaɓar Kalshingi, Alhaji Baba, ya karɓi wasiƙar murabus ɗin Yayari a ranar 12 ga watan Agusta.
Tsagin Turaki ya gabatar da Yayari a matsayin ɗan takararsa na gwamnan Gombe a watan Yunin 2026.
Ficewarsa daga PDP na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida da taƙaddama kan ɗan takarar da zai wakilci jam’iyyar a zaɓen gwamnan jihar na 2027.
Wani ɓangaren PDP ya gabatar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takararsa.
Murabus ɗin Yayari na iya ƙara dagula rikicin PDP a Gombe tare da haifar da tambayoyi kan makomar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a jihar.