Sarkin Musulmi Ya Nemi A Fara Duban Watan Maulidi A Ranar Alhamis

Sarkin Musulmi ya nemi a fara duban watan Maulidi a ranar Alhamis

Majalisar Sarkin Musulmi ta buƙaci Musulmi su sanya ido domin neman jinjirin watan Rabi’ul Awwal 1448 bayan Hijira a ranar Alhamis, 13 ga watan Agusta 2026.

Majalisar ta yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce Alhamis, 13 ga watan Agusta, wadda ta yi daidai da 29 ga Safar 1448 bayan Hijira, ita ce ranar da aka ware domin fara duban jinjirin watan Rabi’ul Awwal.

Majalisar ta buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan da ya sanar da shugaban gundumarsa ko shugaban ƙauyen mafi kusa da shi.

Daga nan za a isar da bayanin ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya.

Rabi’ul Awwal wata ne mai muhimmanci a kalandar Musulunci.

Musulmi da dama suna gudanar da bukukuwa a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, domin tunawa da ranar haihuwar Fiyayyen Hallita, Annabi Muhammad (SAW).

Ana yin bikin Mauludi, karatun Alƙur’ani, wa’azi, yabo ga Annabi da sauran ayyukan ibada domin tunawa da wannan rana.

Majalisar ta yi addu’ar fara watan Rabi’ul Awwal 1448 cikin nasara.

Comments (0)
Add Comment