’Yan Bindiga Sun Kashe Wani da Yaron Dan Uwansa, Sun Sace Mutum 11 A Sakkwato

’Yan bindiga sun kashe wani da yaron ɗan uwansa, sun sace mutum 11 a Sakkwato

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu 11 a hare-hare daban-daban da suka kai a ƙauyukan Taloka da Huda, da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo ta Jihar Sakkwato.

Wani mazaunin Taloka ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar, waɗanda suke a kan babura kusan 20, sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 12:30 a dare ranar Talata, inda suka rika shiga gidaje ɗaya bayan ɗaya.

Maharan sun yi garkuwa da Alhaji Yusuf, ’yarsa da matar ɗansa.

Sun kuma kashe yaron ɗan uwansa, Abdullahi Dan Almajiri.

Daga nan ’yan bindigar suka shiga wani gida, inda suka yi garkuwa da wasu matan aure biyu, sannan suka tafi da yara biyu; namiji da mace.

Mazaunin yankin, ya ce Alhaji Yusuf ya faɗa wa ’yan bindigar cewa ya tsufa sosai ba shi da ƙarfin da zai iya yin doguwar tafiya.

Nan tanke suka kashe shi suka bar gawarsa a wajen.

Har ila yau, sun kai hari ƙauyen Huda, da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar Litinin, inda suka sace manoma biyar, daga baya suka saki ɗaya daga cikinsu.

Wani mazaunin yankin ya ce wannan shi ne hari na 11 da aka kai wa al’ummar.

Ya ce a baya ’yan bindigar sun kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da mutane 46, waɗanda aka sake bayan an biya Naira miliyan 12 da babura uku a matsayin kuɗin fansa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce bai samu labarin hare-haren ba.

Amma ya ce zai yi ƙarin bayani da zarar ya samu labarin abin da ya faru.

Comments (0)
Add Comment