Gwamnatin Sokoto za ta raba wa jami’an tsaro babura 1,000 domin inganta tsaro
Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 1,759,250,000 domin sayen babura ƙirar Bajaj guda 1,000 da za a raba wa hukumomin tsaro a jihar, domin ƙarfafa yaƙi da ƴanbindiga.
A cewar daraktan janar na yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, an amince da wannan buƙatar ne a majalisar zartarwar jihar.
Bawa ya ce, “Sayen babura guda 1,000 na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin ƙara wa jami’an tsaro kayan aiki da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu a wuraren da matsalar ƴanbindiga ta fi ƙamari.”
Ya ƙara da cewa sayen baburan zai kasance ƙarin tallafi ne ga motocin yaƙi masu sulke guda 62 da gwamnatin jihar ta saya kwanan nan, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 27.
A cewar Bawa, “Gwamnatin jihar ta riga ta samar da motocin sulke guda 62 da aka raba wa hukumomin tsaro, kuma wannan sabon shirin na sayen babura zai ƙara ƙarfafa ayyukan sintiri da sauran ayyukan tabbatar da tsaro.”
Baya ga batun tsaro, Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da wasu ayyuka da dama da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, samar da ruwa da bunƙasa sana’o’i.
Daga cikin ayyukan akwai ware Naira miliyan 723,171,671.23 domin gyara makarantar Government Technical College da ke Runjin Sambo, yayin da aka amince da kashe Naira miliyan 498,995,000 domin gyaran A.A. Raji Special School.
Haka kuma, an ware Naira miliyan 489,319,380 domin gyaran kashi na farko na College of Nursing Sciences, sannan Naira miliyan 229,363,455 domin gyaran dakunan kwanan dalibai maza da mata na College of Basic and Remedial Studies.
A fannin noma, an amince da Naira miliyan 174,642,000 domin gyaran gidajen ma’aikata da inganta katangar College of Agriculture and Animal Science da ke Wurno.
Majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 133,665,861.32 domin gina katangar Wamakko Primary Health Centre.
A kokarin ƙarfafa sana’o’in mata, gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 93,880,000 domin sayen kayan koyon sana’a ga cibiyoyin koyon sana’a na mata guda 46 da ke faɗin ƙananan hukumomi 23 na jihar.