Tinubu Ya Aminice da Farfaɗo da Rijiyoyin Man Fetur da Ke Tsakiyar Teku

Tinubu ya aminice da farfaɗo da rijiyoyin man fetur da ke tsakiyar teku

Gwamnatin Najeriya ta amince da wani sabon tsarin haraji da dokoki da nufin farfaɗo da harkar hako man fetur da iskar gas daga rijiyoyin mai da ke tsakiyar teku.

Gwamnatin ta yi imanin cewa matakin zai iya jawo jarin da ya kai dala biliyan 50 cikin harkar mai da gas, tare da ƙara samar da ayyukan yi da kuma kuɗaɗen shiga ga ƙasar.

Babban gwajin wannan sabon tsarin shi ne ko kamfanonin mai za su amince su ci gaba da aikin Bonga South West-Aparo, wani shiri da ya kwashe kimanin shekaru 30 ana shirin aiwatar da shi.

Ana sa ran aikin zai buƙaci jarin farko na kusan dala biliyan 10, kuma idan aka kammala shi zai iya samar da ganga 150,000 na ɗanyen mai a kowace rana.

Gwamnatin Najeriya na sa ido kan ko kamfanin Shell, wanda ke gudanar da rijiyar man Bonga, zai yanke shawarar fara aikin a shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar raguwar saka jari a harkar mai da gas sakamakon satar mai, rashin tsaro da kuma ficewar wasu manyan kamfanonin mai daga wasu rijiyoyin da ke kan tudu.

A lokaci guda, gwamnati na kuma shirin sauya wasu ƙa’idojin rarrabawa da farashin ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida, domin rage musu tsadar samar da mai.

Ana sa ran matakan za su taimaka wajen ƙara yawan man da ake haƙowa da jawo ƙarin jari da kuma tabbatar da cewa ana sarrafa mafi yawan ɗanyen man Najeriya a cikin ƙasar.

Comments (0)
Add Comment