’Yan Sanda Sun Kama ’Yan Bindiga 2, Sun Ceto Dan Shekara 10 A Sakkwato

’Yan sanda sun kama ’yan bindiga 2, sun ceto ɗan shekara 10 a Sakkwato

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, ta kama wasu ’yan bindiga biyu tare da ceto wani yaro ɗan shekara 10 da aka sace.

Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri game da ’yan bindigar da ke addabar wasu sassan jihar, sannan ta kai musu samame tare da kama su.

A wani samame da ’yan sanda suka kai ƙauyen Tudun Doki da ke Ƙaramar Hukumar Gwadabawa, sun kama wani da ake zargi da aikata laifuka mai suna Abdullahi Buba, wanda aka fi sani da “Osho”.

A lokacin gudanar da bincike, Buba ya bayyana cewa yana cikin ’yan bindigar da suka addabi yankunan ƙananan hukumomin Gwadabawa, Kware da Gada.

Rundunar ta ce bayanansa sun taimaka wajen kama wasu daga cikin ’yan bindigar da kuma tarwatsa ƙungiyarsu.

A wani labarin kuma, rundunar ta samu ƙorafi daga Sani Ibrahim na Gidan Madi a Ƙaramar Hukumar Tangaza cewa yaron ɗan uwansa, Sufiyanu Muhammad mai shekaru 10, ya ɓace kuma ba a san inda yake ba.

Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce ’yan sanda sun fara bincike tare da sanya ido kan wasu mutane biyu da aka gan su a kan babur ɗauke da wani buhu.

Ya ce lokacin da mutanen suka fahimci cewa ’yan sanda na bin su, sai suka jefar da buhun suka gudu.

Bayan an buɗe buhun, sai aka gano yaron da ake nema a ciki.

An ceto shi ba tare da wani abu ya same shi ba.

Nan take aka kai yaron asibiti domin duba lafiyarsa.

Bayan duba shi kuma ya samu sauƙi, sai aka sallame shi.

Yaron ya shaida wa ’yan sanda cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da shi ya kai shi wani ɗaki, ya yi masa allura sannan ya saka shi a cikin buhu.

Rundunar ta ce ta kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, wanda ya amsa laifinsa.

Comments (0)
Add Comment