Abin Mamaki: An Bayyana Ɗan Wasan Katsina United Ya Mutu, Sai Aka Same Shi Da Rai A Gidan Ajiye Gawa

Abin Mamaki: An Bayyana Ɗan Wasan Katsina United Ya Mutu, Sai Aka Same Shi Da Rai A Gidan Ajiye Gawa

An shiga rudani kan halin da ɗan wasan baya na Katsina United, Ozor Chinedu, yake ciki bayan ya faɗi yayin wasan sada zumunta da Niger Tornadoes a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina ranar Talata.

Ɗan wasan mai shekaru 18, wanda Katsina United ta ɗauka kwanan nan daga Kano Pillars, ya faɗi a filin wasa yayin gasar Gusau/Ahlan Pre-season Cup, inda aka garzaya da shi asibitin K-Dara Specialist Hospital. Rahotanni sun ce likitoci a asibitin sun bayyana cewa ya rasu.

Bayan hakan, Katsina United ta fitar da saƙon ta’aziyya, yayin da wasu tsoffin kungiyoyin ɗan wasan, ciki har da Heartland da Kano Pillars, suka yi alhinin rasuwarsa a shafukan sada zumunta.

Sai dai lamarin ya ɗauki sabon salo bayan ma’aikatan gidan ajiye gawa na Babban Asibitin Katsina sun lura da motsi a jikin ɗan wasan.

Nan take aka mayar da shi sashen kula da marasa lafiya masu tsanani (ICU), inda aka sanya masa iskar oxygen.

Jami’in hulɗa da manema labarai na Katsina United, Nasir Gide, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa an bayyana ɗan wasan ya mutu har sau biyu kafin daga bisani a gano alamun rai.

Haka kuma, Heartland FC, ɗaya daga cikin tsoffin kungiyoyin da Chinedu ya taɓa bugawa, ta tabbatar da faruwar lamarin tare da roƙon magoya bayanta da su yi masa addu’ar samun lafiya.

Ya zuwa safiyar Laraba, Chinedu yana cikin mummunan hali a Babban Asibitin Katsina, yayin da al’ummar ƙwallon ƙafa ke jiran cikakken rahoton likitoci kan halin da yake ciki.

Comments (0)
Add Comment